12 Agusta 2026 - 22:12
Source: ABNA24
Shin Labaran Marubuta Tarihi Da Gaske Suna Da Inganci?

Tarihi madubi ne don nuna gaskiya mai tarin yawa; duk da cewa a koyaushe hannaye masu ƙazanta suna aiki don canza fuskar wannan madubi mai haske, amma har yanzu tarihi a fage da yawa yana da karbuwa a matsayin tushen ilimi da fahimta; domin tarihi kamar kowane labari yana da ingantacce, mai ƙarfi, mai rauni, da kuma wanda ba a san shi ba. Bugu da ƙari, akwai sassa biyu na tarihi waɗanda suka tsira daga kowane canji: tarihin da ya wanzu a matsayin alamomi na zahiri da na halitta a duniya, wanda mafi girma daga wannan, tarihin da ya zo mana ta hanyar wahayi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahl al-Bayt (AS) - ABNA: Duk da cewa tarihi madubi ne mai girma da ban sha'awa don nuna gaskiya mai tarin yawa, amma cikin baƙin ciki mai yawa, a koyaushe hannaye masu ƙazanta suna aiki don canza fuskar wannan madubi mai haske. Saboda haka, tarihi yana da ƙazanta da yawa waɗanda wani lokacin sanin tsarkakakke daga gurbatacce yakan yi wuya sosai.

Dalilin haka ma a bayyane yake domin a gefe guda marubuta tarihi ba koyaushe ne su ka kasance masu tsaka-tsaki ba; a'a, suna rubuta tarihi yadda suke so bisa ga son rai na kansu ko na ƙungiyarsu, kuma a gefe guda sarakuna masu zalunci a kowane lokaci suna ƙoƙari su mallaki marubuta tarihi, su rubuta abin da suke so su rubuta.

Ko da yake bayan faduwar mulkin kowane ɗayan waɗannan azzalumai, da samun yanayi mafi 'yanci, ana yin ƙoƙari don gyara kurakurai da rama barnar da aka yi a tarihi; amma duk da haka, wani lokacin wannan nasara ba ta samuwa, ko kuma gyare-gyaren bai isa yadda yakamata.

Abin ban sha'awa shi ne, wani lokacin tare da canjin gwamnatoci masu son kai waɗanda ke da ra'ayi daban-daban, al'amuran tarihi suna canzawa sau da yawa. Misali, Bani Umayya sun karkatar da tarihin Musulunci ta wata hanya, Bani Abbas suna zuwa suka canza shi ta wata hanya, magadan Bani Abbas kuma suka sake canza shi ta wata sabuwar hanya.

Wata rana Stalin, mai mulkin kama-karya na Rasha, yana rubuta tarihin juyin juya halin gurguzu yadda yake so; har ma yana koyar da shi a makarantun ƙasar. Washegari magadansa waɗanda suke ganinsa a matsayin mai zubar da jini, suka tattara waɗannan littattafai suka ajiye gefe, suka rubuta tarihin juyin juya halin ta wata hanya dabam, haka kuma kowace ƙungiya da ta hau mulki tana sake rubuta tarihin ƙasar bisa ga son rai da akidarta.

Saboda haka, wasu sun ƙi tarihi sosai har suka faɗi wannan magana sananniya a matsayin azarbabi game da shi cewa shi: "Tarihi, tarin abubuwan da suka faru da labaran da ba su taɓa faruwa ba, game da al'ummomin da ba su taɓa samuwa ba!"

Amma dole ne mu yi adalci cewa duk da waɗannan ƙazanta, har yanzu tarihi a fage da yawa yana da karbuwa a matsayin tushen ilimi da fahimta; domin tarihi kamar kowane labari yana da ingantacce, mai ƙarfi, mai rauni, da kuma wanda ba a san shi ba.

Labaran tarihi da suka tabbata game da mutane kamar rundunar Mongol da Hitler da abubuwan da suka faru marasa dadi na Andalus da ɗaruruwan makamantansu ba za a iya musanta su ba. Abin da ya fi shiga cikin musu da tabbatarwa da zargi su ne sassan cikakkun bayanai na tarihi, waɗanda idan kuma aka tabbatar da su ta hanyar labaran masu ƙarfi, suna iya samun karbuwa; duk da ba shakka labarai marasa ƙarfi masu rauni ma ba fa ‘yan kadan ba ne suna da yawa.

Wannan hukunci ne na adalci game da tarihi; don haka bai kamata mu rufe ido da kunne mu karɓi duk abin da aka faɗa ba, kuma ba kuma mu sanya layin rushewa a kan dukkan littattafan tarihi ba.

Bugu da ƙari, akwai sassa biyu na tarihi waɗanda suka tsira daga kowane canji: tarihin da ya wanzu a matsayin alamomi na zahiri da na halitta a duniya, waɗanda ba za’a kawar d su cikin sauƙi ko karkatar da su ba, kuma Alkur'ani mai girma ya dogara sosai a kan wannan bangare, kuma ayoyin tafiya a cikin ƙasa don sanin tarihin magabata suna nuni ga wannan bangare. Kuma mafi girma daga wannan, tarihin da ya zo mana ta hanyar wahayi, kamar tarihin Alkur'ani wanda yake tsarkakakke kuma mai inganci. A gaskiya, kamar yadda mafi kyawun mai yin doka shine Allah, haka ma mafi kyawun mai rubuta tarihi shi ne; domin Ya mallaki dukkan cikakkun bayanai kuma son rai na mutum ko ƙungiya ba shi da ma'ana a gare Shi, kuma tare da waɗannan sharuɗɗa guda biyu na asali, Shi ne mafi kyau fiye da kowa wajen ba da labarin tarihi.

Abin ban sha'awa shi ne, Alkur'ani mai girma wani lokacin yana maimaita wani labari na tarihi sau da yawa. Wasu suna mamakin me yasa, misali, labarin Nuhu (AS) ko Musa (AS) da Fir'auna, da fuskantar waɗannan Annabawa da masu kama-karya da azzalumai an maimaita su sosai, ba tare da sanin cewa kowane ɗayan waɗannan ayoyin yana dubi ga waɗannan abubuwan tarihi ta wani fage ba; domin wani lamari na tarihi wani lokacin yana da fage da yawa.

Misali, game da tarihin Bani Isra'ila, wani lokacin muna kallonsa ta fagen yaƙi da azzalumin lokaci, wani lokacin ta fagen taurin kai na wannan al'umma masu taurin kai, wani lokacin muna ganin sakamakon rashin haɗin kai a tsakaninsu, wani lokacin kuma sakamakon rashin godiya da nuna ƙin yarda ga ni'imominn Allah Ta’ala.

A taƙaice, abubuwa da yawa na tarihi suna kama da madubai masu fage da yawa, kowanne yana haskaka wata gaskiya ne. (1)

Madogara:

(1) Littafin "Sakon Alkur'ani," Makarim Shirazi, Nasir, Darul-Kutubil-Islamiyyah, Tehran, 2007 (1386 AH), bugu na 9, juz'i na 1, shafi na 173.

.......................................

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha